A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, taron ya gudana ne ranar Laraba, 7 ga watan Janairu 2026 (daidai da 17 ga watan Rajab 1447) domin karrama babban malami, Ayatullah Sayyid Muhammad Tabataba'i, wanda aka fi sani da "Sayyid al-Mujahid".
Wannan taro ne na hadin gwiwa tsakanin Haramin Hazrat Abbas (AS), Babban Kwamitin Rayar da Gidajen Gado, da kuma Cibiyar Bincike ta Sheikh Tusi. Za a ci gaba da taron a rana ta biyu (Alhamis) a birnin Karbala.
Kololuwar bikin buɗe taron ita ce ƙaddamar da wasu manyan kundaye guda biyu masu cike da tarihi, waɗanda sakamakon binciken shekaru masu yawa ne na wasu fitattun masu bincike. Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Ahmad al-Safi, wakilin shari'a na Haramin Hazrat Abbas (AS), ya kaddamar da waɗannan ayyuka guda biyu a cikin wani biki mai cike da daraja:"
"Mausu’atul 'Al-Manahil': Wannan kundin fikihu ne da Sayyid al-Mujahid ya wallafa, wanda a ƙarshe zai kai kusan mujalladi hamsin (50). A wannan biki, an ƙaddamar da mujalladi goma sha takwas (18) na farko, tare da ƙarin kundi guda ɗaya na gabatarwa daki-daki wanda ke bayani kan littafin da kuma marubucin.
Mausu’atu "Al-Sayyid al-Mujahid wa Turasuhu al-Ilmi": Wannan kundin bincike ne mai dauke da mujalladi 22. Ya kunshi gyaran rubuce-rubucen Sayyid al-Mujahid, nazari kan tunaninsa, da kuma makaloli daga masana na kasashen Iran, Lebanon, Kuwait, da Iraki.
A yayin jawabin sa, Sayyid Ahmad al-Safi ya yaba da matsayin ilimi da na jihadi na Sayyid al-Mujahid. Babban jigon jawabinsa shi ne yin gargadi mai tsanani game da hadurran da ke barazana ga tsofaffin littattafan hannu na malamai, inda ya jaddada muhimmancin kiyaye su domin kare martabar ilimin musulunci.
Your Comment